Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A na sa ran majalisar dattijai zata tantance babban mai rikon mukamin jojin Najeriya

Published

on

Ana kyautata zaton cewa a yau ne ake saran cewa majalisar datijjai zata tatance mai rikon mukamin babban jojin Najeriya Maishari’a Tanko Muhammad wanda a makon jiya ne fadar shugaban kasa ta aike da sunan majalisar don neman sahalewar su.

 

Mai shari’a Tanko Muhammad wanda yake rike da mukamin mai rikon babban jojin Najeriya bayan da aka dakatar da tsohon babban jojin Najeriya Walter Samuel Onneghen bayan da aka yi zargin sa da bayar da bayanan karya kan kadarorin da ya mallaka.

 

A dai makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sunan mai rikon babban jojin Najeriya don tantance kamar yadda sashi na 23 daya cikin baka na kundin tsarin mulkin shekara ta 1999 ya tanada.

 

An dai aike da sunan Tanko Muhammad ne ga majalisar bisa irin shawarwarin da hukumar kula da shari’a ta kasa NJC ta bada kan nadin nasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!