Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

APC: ta zargi kwamishinan yan sandan kano da hada baki da jamiyyar PDP domin murda zaben gwamna

Published

on

Jam’iyyar APC ta zargi kwamishinan yan sandan jihar Kano Muhammad Wakili da hada baki da jam’iyyar PDP wajen ganin an murda zaben Gwamnan a jihar nan.

Jami’in yadda labaran jam’iyyar ta APC na kasa Malam Lanre Issa Onilu ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin jiya a birnin tarayya Abuja.

Ta cikin sanarwar jam’iyyar ta zargi kwamishinan yan sandan Muhammad Wakili da ketare iyaka ta hanyar wu ce makadai da rawa a cikni ayyukan sa.

Sanarwar ta kara da cewa, suna da bayanan da ke nuni da cewa kwamishinan ya taimakawa jam’iyyar ta PDP wajen aringizon kuri’u, ta hanyar baiwa wadanda suke yan gaba-dai gaba dai din kwankwaso kariya ta musamman amma ya ki  baiwa kwamishi nan a kano kariya.

Ya kuma ce jam’’iyyar APC ce jam’iyyar al’ummar Kano, kuma jam’iyyar na da karfin gwiwar za ta lashe zaben da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!