Kiwon Lafiya
Asusun lamuna ya shawarci Najeriya samar da hanyoyin bunkasa kudaden shiga
Asusun bada lamuni na majalisar dinkin duniya IMF ya shawarci kasar nan da ta lalubo hanyoyin da za ta bunkasa kudaden shigar ta musaman ta bangaren da ba na mai ba.
Mataimakin daraktan da ke kula da bangaren tara kudade na asusun na IMF Poulo Mauro ne ya bayyana hakan ya yin taron hukumar ta IMF da kuma bankin duniya da ke gudana a birnin Bali na kasar Indonesia.
Ya ce kasar nan ba bukatar sauya dabarun tara kudaden ta daga bangaren mai zuwa wasu bangare na daban sai dai ya ce hakan ba yana nufin kasar nan ta yi hakan da gaggawa ba amma dai akwai bukatar hakan.
Mauro yana wadannan kalamai ne yayin da ya ke maida jawabi kan tambayar da aka yi masa na cewar wace hanya kasar nan zata bi wajen habaka kudaden harajin ta.
Inda kuma ya amsa da cewar bunkusa bangaren da ba na albarkatun man fetur ba na da matukar muhimmanci, a cewar sa ya kamata a sanya jari mai yawa a bangaren masana’antu da noma