Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba mu da masaniyar bayar da kwangilar samar da magunguna a kano – Gwamna Abba

Published

on

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace bashi da masaniyar bayar da kwangilar samar da magunguna a ƙananan hukumomi 44 dake faɗin Jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya musanta labarin da ake yaɗawa na kwangilar da aka ce an bayar a kwanan nan domin samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye da Babban Daraktan yaɗa labaran gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Ta cikin sanarwar gwamnan ya umurci Shugaban Hukumar karɓar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da rashawa ta Jihar Kano da ta gaggauta bincikar wannan zargi tare da bayar da rahoton sakamako domin ci gaba da ɗaukar matakin da ya dace.

Gwamna Abba ya bukaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba dayin hakuri har sai an kammala bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!