Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ba mu taɓa samun ƙorafi kan gine filayen makarantun gwamnati ba – Kwamishinan Ilimi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, bata taɓa samun ƙorafi kan gini filayen makarantun gwamnati ba.

Kwamishinan ilimi Malam Muhammad Sanusi Sa’idu Ƙiru ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

Ƙiru ya ce, ma’aikatar ilimin ba ta da masaniya a kan shagunan da ake ginawa a filayen wasu daga cikin makarantun gwamnati.

Dalilan da suka sanya muka janye malamai – Ƙiru

“Har yanzu ba mu taɓa samun ƙorafi kan gina shaguna a wasu daga cikin filayen makarantun gwamnati ba, kuma ba mu da masaniya kan hakan’ a cewar Ƙiru.

Kwamishinan ya kuma ce ma’aikatar ilimi ta hana karɓar kuɗi hannu da hannu a duk ma’aikatun dake karkashin ma’aikatar ilimi,m sai dai aje asusun karɓar haraji a biya a can.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!