Connect with us

Labarai

Barayi sun sace naira miliyan 16 a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina

Published

on

Wasu da ake zargin barayi ne sun fasa ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa tare da sace makudan kudade da ya kai naira miliyan goma sha shida (16).

Rahotanni sun ce barayin sun shiga ofishin sakataren gwamnatin jihar na Katsina ne da ke sakatariyar gwamnatin jihar a daren shekaran jiya Lahadi.

Wata majiya a ofishin sakataren gwamnatin jihar ta shaidawa manema labarai cewa, kudaden da barayin su ka sace ka iya zarce yadda aka sanar.

‘‘Tuni ma jami’an ‘Yan sanda sun kama wasu daga cikin ma’aikatan ofishin sakataren gwamnatin jihar ta Katsina, ciki kuwa har da mai gadi da kuma wasu jami’an gwamnati biyu da ke aiki a ofishin’’. A cewar majiyar.

Katsina: An ceto wasu mata da aka yi garkuwa da su

Gwamnan Katsina ya jagoranci tawagar haduwa da takwarorinsu na Kasar Nijar

Katsina:Jiragen helkwabta ne ke jefo makamai inji wani da ke zargi dan bindiga dadi

Haka zalika majiyar ta kuma ce kudaden wani bangare ne na kudaden alawus-alawus na ma’aikatan wucin gadi da ke koyarwa a makarantun Firamare da Sakandire ta cikin shirin samar da aikin yi na jihar ta Katsina wato ‘S-Power’.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,158 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!