Labarai
Buhari zai gabatarwa majalisa kasafin ƙudi na 2022

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatarwa majalisa dabtarin kasafin kuɗin shekarar 2022.
A ranar Alhamis ne dai shugaba Buhari zai gabatar da kasafin a gaban majalisun kasar nan.
Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege, ne ya shaida hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Ovie Omo-Agege ya bukaci kwamitin harkokin kudi na majalisar da ya gaggauta aikin da yake yi kan tsare-tsaren kasafi da kudade, domin gabatar da rahotonsa a gaban majalisar a ranar Laraba.
You must be logged in to post a comment Login