Labarai
Duk da matsalar tsaro: Buhari zai tafi Turkiyya kan batun kasuwanci
A yau Alhamis ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya.
Shugaba Buhari zai halarci taron haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka karo na uku wanda shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai karɓi baƙuncin sa.
Malam Garba Shehu, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Tarin zai yi nazari kan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da Turkiyya da kuma batun kasuwanci da yarjejeniyar makamashi tun bayan taron ƙarshe da aka gudanar a shekarar 2014.
Shugaba Buhari zai samu rakiyar uwargidansa Hajiya Aisha Buhari da ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama da na Tsaro Man-Genjo janar Bashir Magashi mai ritaya da na Lafiya Dakta Osagie Ehanire sai na Noma Mohammed Abubakar da na Masana’antu Ciniki da Zuba Jari Adeniyi Adebayo.
Sauran sun haɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo janar Babagana Monguno mai ritaya da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta ƙasa Ambasada Ahmed Rufa’i.
You must be logged in to post a comment Login