Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba ya ƙaddamar da biyan ƴan Fansho Naira biliyan 5000 a karo na biyu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da bayar da kuɗin garatuti kashi na biyu ga tsaffin ma’aikatan da suka kammaka aikin su 4000 domin zuwa su gudanar da sana’o’in dogaro dakai.

Da yake ƙaddamar da bayar da kuɗin garatutin yau a fadar gwamnatin Kano, gwamna Abba Kabir Yusuf yayi kira ga dukkanin wa’inda suka karɓi wannan kudin a wannan lokaci da su tabbatar sunje gida domin kula da iyali da su.

Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa Wannan kuɗi da suka karɓa hakkin su ne ba kyauta aka basu ba, irin halin da suke ciki na tsahon shekaru da kammala aiki ba’a biya su ba ya sanya gwamnati tayi wannan yunkurin domin biyan su hakkin su.

Haka kuma gwamnatin jihar Kano tace zata ci gaba da biyan dukkannin ƴan fansho rukuni rukuni kuɗaɗen su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!