Labarai
Gwamna Abba ya ƙaddamar da dashen bishiyoyi sama da miliyan 3 a jihar Kano
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da dasa bishiyoyi sama da miliyan uku domin samarwa da jihar kano yanayi mai kyau musamman kyaucewa daga faɗawa yayin kwararowar hamada da zaizayar ƙasa da dai sauran abubuwa da suke da alaƙa da hakan.
Da yake ƙaddamarwa gwamna Abba Kabir Yusuf ya shawarci al’umma da su kasance masu mayar da hankali wajen dashen bishiyoyi a dukkanin lunguna da saƙo na jihar Kano domin samar da kyakkyawan yanayi.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa gwamnatin sa zata samar da tsirrai da za’a a raba ga al’umma a dukkanin lunguna da saƙo dake faɗin jihar kano.
Gwamnan ya ƙara da cewa yana kira ga al’umma musamman a guraren da ka dasa bishiyoyin nan da su kasance masu ban ruwa gare su ko da bayan damina.
Da yake jawabi sarkin kano na sha shida Khalifa Muhammadu Sunusi II yayi kira ga al’umma da masu jagorantar al’umma da su mayar da hankali wajen dashen bishiyoyi a gidajen su.
A yayin taron an shawarci al’ummar da su ci gaba da sanya bishiyoyi a cikin gidajen su da bakin hanya.
You must be logged in to post a comment Login