Labarai
Gwamna Abba ya aikewa da majalisar dokokin kano sunayen mutane 6 da za’a naɗa Kwamishina
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya aikewa majalisar dokokin Kano da sunayen mutane 6 domin ta amince masa ya naɗa su a matsayin kwamishinoni a jihar nan.
DA yake karanto wasikar a zauren majalisar, kakakin majalisar Jibril Isma’il Falgore yace tantance waɗanda gwamnan ya turo da amincewa dasu Idan sun cancanta zai taimaka wajen tafiyar da Mulki cikin sauki.
Sunayen wadanda aka aikewa majalisar sun hada da Shehu wada Sagagi, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, Dr Isma’il Dan Maraya, Dahiru Mohd Hashim, Dr Injiniya Gaddafi Sani Shehu, Kwamared Abdulkadir AbdulSalam.
Gwamnan Abba Kabir Yusif ya aikewa da majalisar dokokin Kano wasikar neman yin gyara akan kasafin kudin shekara ta 2024 da muke bankwana da ita domin cike gibin kudin da yawansu ya zarce naira biliyan 66.
Da yake karanto wasikar, Kakakin majalisarJibril Isma’il Falgore yace zasu yi bakin ƙoƙarin su domin yin gyaran dokar.
Sai dai da yake Ƙarin bayani ga manema labarai, shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala yace majalisar zata gaggauta gyaran dokar kasafin kudin na shekarar da take fita domin samun damar cike gibin kudaden.
Dala ya Kuma yi Karin bayani akan sunayen mutanen da da gwamna Abba Kabir Yusif ya aikewa majalisar domin basu ragamar tafiyar hukumar Zakka da Hubusi ta jihar nan da Kuma hukumar Shari’a.
A-Civil Service Commission
1. Engr. Ahmad Ishaq – Chairman
2. Alh. Abdullahi Mahmoud – Permanent Member I
3. Ado Ahmed Mohammed – Permanent Member II
Hukumar Sharia
1. Sheikh Abbas Abubakar Daneji – Executive Chairman
2. Mallam Hadi Gwani Dahiru – Permanent Commissioner I
3. Sheikh Ali Dan’Abba – Permanent Commissioner II
4. Mallam Adamu Ibrahim – Member
5. Mallam Abubakar Ibrahim Mai Ashafa – Member
6. Mallam Naziru Saminu Dorayi – Member
7. Sheikh Kawu Aliyu Harazumi – Member
8. Sheikh Mukhtar Mama – Member
9. Sheikh Ibrahim Inuwa Limamin Ja’en – Member
10. Sheikh Dr. Sani Ashir – Secretary/Member
Hukumar Zakkat da Hubsi sune kamar haka
1. Barr. Habibu Dan Almajiri – Executive Chairman
2. Sheikh Nafiu Umar Harazumi – Permanent Commissioner I
3. Dr. Ali Quraish – Permanent Commissioner II
4. Mallam Abdullahi Sarkin Sharifai – Member
5. Mallam Adamu Muhammad Andawo – Member
6. Mallam Yahaya Muhammad Kwana Hudu – Member
7. Sheikh Hassan Sani Kafinga – Member
8. Sheikh Arabi Tudun-Nufawa – Member
9. Mallam Sani Shariff Umar Bichi – Member
10. To Be Filled by CSC – Secretary
Haka kuma majalisar ta bukaci waɗanda gwamnan ya aikewa majalisar domin nadawa a shugabancin hukumar Zakkar da Shari’a dasu bayyana a gabanta a ranar larabar nan Mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login