Labarai
Gwamna Abba ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2024 ya zama doka
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar, jimillar kasafin kuɗi Naira biliyan 437 a matsayin kasafin kudin shekarar 2024. An rattaba hannu kan kudurin kasafin ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da shi.
A wata sanarwa da Babba Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce kasafin ya kunshi kashi 64 cikin 100 na kudaden da ake kashewa da kuma kashi 36 bisa 100 na yau da kullum. Kasafin kudin da aka rattaba hannu anyi mai lakabin “Budget of Restoration and Transformation”.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wani muhimmin taro da aka gudanar a gidan gwamnati, Gwamna Yusuf ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa za a yi amfani da kasafin kudin cikin adalci domin amfanin al’umma bisa yadda ake tafiyar da harkokin kudaden gwamnati.
Ya jaddada cewa wannan muhimmin lamari ne da ke da matukar tasiri ga rayuwar kowane dan kasa a cikin jihar da kuma wajenta.
“Ina so in ba da tabbacin cewa ware kashi 64% na kasafin kudin ga manyan ayyuka da kuma kashi 36% na kashe kudade na yau da kullun zai yi tasiri ga rayuwar ‘yan kasa.”
“Jimillar kiyasin kasafin da aka amince da shi a yau ya kai 437,338,312,787.83, inda aka ware kaso 64% ga manyan ayyuka da ya kai 379,835,94,351, da kuma kashe-kashen da ake kashewa akai-akai ya kai 456,503,218,483.73.”
“A yau mun shaida amincewa da kasafin kudin shekarar 2024, wanda aka gabatar wa majalisar dokokin jihar Kano watanni uku da suka gabata.
“Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga kakakin majalisar dokokin jihar Kano bisa jajircewarsa na ganin kasafin kudin ya tabbata.
You must be logged in to post a comment Login