Connect with us

Manyan Labarai

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Published

on

Gwamnan Jihar Kano Abdullah Umar Ganduje ya sanar da nadin Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi II a matsayin shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano.

A wata sanarwa da sakataran yada labarai na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Abba Anwar ya fitar tace nadin Malam Muhammad Sunusi II zai fara aiki daga ranar litinin 9 ga watan Disambar da muke ciki.

Sanarwar tace sauran Sarakunan da Gwamnatin Kano ta kirkiro da suka hada da Sarkin Rano Tafida Abubakar ILa da Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II da Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero Mambobi ne na sabuwar majalisar Sarakunan ta Jihar Kano.

Sanarwar da Abba Anwar ya fitar ta kara da cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci shugaban majalisar Sarakunan Jihar ta Kano kuma Sarkin Kano da ya kaddamar da sabuwar majalisar Sarakunan da Gwamnatin ta kikiro.

Shi dai shugabancin majalisar Sarakunan ta Jihar Kano zai rika zagayawa ne duk bayan shekaru biyu tsakanin Sarakunan na Jihar Kano.

Daga yanzu Malam Muhammad Sunusi II zai shugabanci majalisar Sarakunan daga nan zuwa shekarar 2021.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,761 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!