Labarai
Gwamnan kano ya sake aikewa da majalisar dokokin jihar ƙarin Kwamishina guda 1
Gwamnan jihar Kano ya sake aikewa da ƙarin sunan Kwamishina guda ɗaya cikin guda shida da aka aikewa majalisar dokokin kano a jiya Litinin.
Da yake karanta wasikar yau a zauren Majalisar kakakin majalisar Jibrin Isma’il Falgore yace ƙarin Kwamishinan cikin shidan da gwamna ya turo ya biyo bayan amincewa tare da tantancewa domin naɗa shi a matsayin mamba na majalisar zartarwa ta jihar Kano domin aiwatar da gwamnati.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya turo da suna Nura Iro Ma’aji a matsayin sabon wanda za’a ƙara tantancewa a matsayin jerin Kwamishinoni.
You must be logged in to post a comment Login