Labarai
Gwamnan Kano ya yi Allah-wadai kan cewa ya yi yarjejeniya da APC kafin yanke hukunci
Gwamnan Ya yaba da rashin katsalandan da Shugaba Tinubu ya yi da bangaren shari’a kan karar zaben Gwamnan Kano.
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi Allah-wadai da yadda akace ya kulla wata yarjejeniya da fadar shugaban kasa kafin ranar 12 ga watan Junairu, 2024 da kotun koli ta yanke hukunci kan karar zaben Kano inda ya samu nasara.
Wannan na ƙunshe ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ta bayyana wata takarda da tuni ta ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke nuni da yarjejeniyar wa’adi hudu tsakanin Gwamna da fadar shugaban kasa a matsayin ba gaskiya ba ce.
Yarjejeniyar ƙarya da ke cewa Gwamna Yusuf ya amince ya tsallaka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, da kuma ikirarin cewa a rusa ko kuma a kyale masarautu biyar, dakatar da rushe gine-gine da kafa majalisar dattawan Kano.
Gwamna ya kuma bayyana cewa, kasancewar ya samu nasarar zabensa ta hanyar kuri’un mutanen Kano, kuma sun tabbatar da hukuncin kotun koli, ba zai tsoratar da duk wani dan siyasa ba.
Bari in kuma tunatar da ma’aikatan siyasa da ke fakewa a karkashin shugaban kasa cewa duk wani hukunci ko alkiblar siyasa da za’a bi a Kano, za’a tabbatar da shi ne a cikin tsarin doka da ikon zartarwa da aka bai wa ofishin Gwamnan.
Mun karyata jita-jitar da ake ta yadawa cewa babu wani da zai dauke hankalin Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen gabatar da ayyuka da shirye-shiryensa na alheri ga al’ummar Jihar Kano.
Har ila yau, ya kamata a lura da cewa kafa majalisar dattawan Kano wani shiri ne na kashin kai na Gwamna, wanda ke da nufin lalubo hanyoyin warware duk wasu matsalolin da za a iya magance su da suka shafi ci gaban zamantakewa da tattalin arziki da siyasa na jihar. Don haka Gwamna Yusuf bai fuskanci matsin lamba kan ya kafa majalisar ba.
“An ja hankalinmu kan wata mummunar fahimta da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta da ke nuni da wata yarjejeniya tsakanin fadar shugaban kasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan hukuncin kotun koli da ta tabbatar da Gwamnan.
“Ina so in bayyana cewa Gwamna Yusuf bai shiga wata yarjejeniya ko sharadi da kowa ba a gaban hukuncin kotun koli, don haka ina kira ga jama’a da su yi watsi da wannan karyar da ake shiryawa.
“Ya ubangijina, alkalan kotun koli sun yi wani muhimmin hukunci cikin adalci da gaskiya da kuma kare mutuncin bangaren shari’a. “
You must be logged in to post a comment Login