Labarai
Gwamnati ta ce akwai yiwuwar sassauta haramci shigo da motoci kan iyakokin kasar nan
Gwamnatin tarayya ta ce akwai me yiwuwar za ta sassauta haramcin da ta yi na shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan da bana ruwa ba.
A watan Janairun shekarar dubu biyu da goma sha bakwai ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin haramta shigo da shinkafa ta kan iyakokin kasar nan da bana ruwa ba.
Shugaban Hukumar kula da shige da fice ta kasa kanal Hamid Ali mai ritaya ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan wani sabon tsari da Hukumar shige da fice ta kasar nan ta yi da takwararta ta jamhuriyar Benin kan musayar bayanai game da kididdigar motoci da ke shigowa ta kan iyakokin kasar nan da bana ruwa ba.
Kanal Hamid Ali wanda ya samu wakilcin mataimakin babban kwanturola na kasa mai kula da harkokin bayanai da fasahar sadarwa Benjamin Aber, ya ce da zaran an kammala shirin akwai me yiwuwar daga haramcin shigo da motoci ta kan iyakoki da bana ruwa ba.