Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

An Tashi Lafiya

Ambaliya: Gwamnatin jigawa ta kawo manyan injina domin daƙile afkuwar ambaliyar ruwa a Jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara shirye-shirye domin daƙile ambaliyar ruwa a faɗin jihar.

Mai bawa Gwamnan Jihar Jigawa shawara a kan cigaban al’umma Hon Hamza Muhammad Jigawa Hadeja, yace tuni dai gwamnatin Jihar ta kawo manyan injina domin zuƙe ruwa a koguna da kuma kududdufai, domin gudin kara samun ambaliyar ruwa kamar yadda ta afku a bara.

Ya kuma ƙara da cewa, “zamu je muga yanayin Tiga, zamuga yanayin Chalawa, da Bagauda za kuma muje wudil muga yanayin tafiyar ruwa. Domin mu bawa gwamnati shawara domin ta ga abin da ya dace ta yi”

Ya kuma gargaɗi ɓata gari, masu cire jingar da ake kafawa a gaɓar kogi, domin kare afkuwar ambaliyar ruwa, cewa “duk wanda aka kama da wannan mummunan aikin, to kuwa zai fuskanci hukunci.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!