Labarai
Gwamnatin jihar Adamawa za ta kara yawan jami’an tsaro a wuraren da ake fama da matsalolin tsaro
Gwamnatin jihar Adamawa ta ce za ta kara yawan jami’an tsaro a wuraren da ake fama da matsalolin tsaro a fadin jihar domin kare rayukan al’umma.
Kwamishinan yada labaran jihar ta Adamawa Alhaji Ahmad Sajoh shi ne ya sanar da haka ga manema labarai a Yolan jihar Adamawa inda ya ce gwamnatin ta dauki wannan mataki ne jim kadan bayan kammala taron gaggawa da jami’an tsaro a jihar domin magance matsalar da ya gudana a jiya Laraba.
Ahmad Sojon ya ce taron wanda mataimakin gwamnan jihar Martins Babble ya jagoranta ya amince da cewa ya kamata a dauki matakin gaggawa domin magance matsalolin da ke addabar jihar.
A cewar sa an kuma umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar da kuma ma’aikatar lafiya da su samar da abinci da kayan magun-guna ga yankunan da rikicin ya shafa.
Rahotanni sun yi nuni da cewa jihar da Adamawa na fama da rikicin Fulani Makiyaya da manoma musamman a kananan hukumomin Guyuk da Demsa da kuma Numan.