Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatin jihar Bauchi ta kori shugaban makaranta

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta sauke shugaban makarantar  Sakandiren hadaka ta Hassan Usman Katsina sakamakon hana daliban makarantar isashshan abinci.

Kwamishinan ilimi na jahar ta Bauchi Dr Aliyu Usman Tilde ne ya sauke shugaban makarantar.

Tube shugaban makarantar da kwamishinan ilimin yayi ,ya shafi wasu masu kula da rumubun ajiye kayayyakin abinci na makarantar su biyu .

Shi dai kwamishinan ilimin na jahar ta Bauchin  DR Usman  Aliyu Tilde ya alakanta sauke shugaban makarantar sakandiren hadakar dake jahar sakamakon ciyar da dalibai dubu daya da dari biyu abincin da ya kamata a ciyar da dalibai dari uku da hamsin.

Dr Aliyu Usman Tilde dai bai fadi sunan shugaban makarantar ba yace yayi mamakin abunda shugaban makarantar ya aikata duk da cewa Gwamnatin jahar ta Kaduna ta samar da isashshan abinci ga makarantun kwanan jahar 35 tun fara zangon karatu na farkon shekarar bana.

Tuni dai kwamishinan ilimin na jahar ta Bauchi ya nada sabon shugaban makarantar mai suna Hamza Dakusni inda aka nada Shamsudden Yunusa a matsayin mai taimaka masa a bangaren mulki.

Yace kwanannan zaa kafa kwamiti da zai ke duba yadda ake rabawa dalibai abinci a makarantun kwanan jahar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!