Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta amince da dokar dawo da masarautu hudu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta amince da sabuwar dokar da za ta tabbatar da dawo da masarautu guda hudu da ta kirkira wanda a kwanakin baya kotu ta rushe su.

A wata sanarwa da kwamshinan labarai Muhammad Garba ya fitar a safiyar yau, ya ce majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da kudirin dokar kirkirar masarautu ta 2019 wacce ta bada damar kara masarautu a jihar kano.

Mal Garba ya ce tuni majalisar ta amince da kafa masarautun da suka hadar da Bichi da ta Karaye da Rano da kuma ta Gaya,  sannan ta kuma aikwa majalisar domin tayi aiki a kai.

Ya ce wasu daga cikin masarautun sun fi na Kano dadewa, kuma anyi kokarin dawo da su a jamhuriyya ta biyu amma hakan bai ya yiwuwa ba.

Yayin da majalisar ta tattauna batutuwa na tsawon shekaru, na yiwuwar sake kafa masarautun a wani yunkurin da take ganin zai kawo cigaban jihar Kano.

Sanarwa ta kara da cewar hakan zai baiwa al’ummar Kano damar kusantar masarautunsu tare da mika bukatun nasu, baya ga bunkasa tattalin arzikin kasa da hakan zai haifar.

Kwamishinan ya kara da cewa bayar da ilimi kyauta da ciyarwa da ake yiwa dalibai na bukatar damawar masarautu domin tabbatar da hakan cikin sauki.

Ya kuma ce dokar samar da wadannan masarautu ta 2019 wanda aka gyara ta domin jin dadin al’ummar jihar Kano, ya biyo bayan rushe masarautun da kotu tayi bayan da tace an mika kudirin dokar ne a sirranci ta hannu mutum daya ba da yarda ko amincewar yan majlisar ba.

Majalisar ta bukaci majalisar dokokin jihar Kano da ta duba kudirin nasu ta kuma lura da jin dadin al’ummar ta domin tabbatar da masarautun.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!