Labarai
Gwamnatin kano ta bayar da tallafi ga iyalan sojoji ƴan kano da aka hallaka a Delta
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin kayan abinci da kuɗi ga iyalan sojoji ƴan asalin jihar Kano da aka hallaka watannin baya a jihar Delta yayin da suke kan aikin su da kwantar da tarzoma.
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da tallafin ga iyalan Laftanar Kanar Abdullahi Hassan Ali da wasu sojoji uku da aka hallaka su tare.
Da yake bayar da tallafin a madadin Gwamnan jihar Babban Daraktan Ayyuka na Musamman ga gwamnatin kano AVM Ibrahim Umaru mai murabus ya ce an dauki wannan mataki ne domin a tallafa wa iyalan sojojin da suka rasu tare da yabawa da irin gudunmawar da suka bayar wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Delta dama ƙasa baki ɗaya.
Da suke jawabi iyalan da suka anfana da Wannan tallafin sun yabawa Gwamna jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa irin kulawa da tausayawa da kuma karamcin da aka nuna musu a lokacin jimamin ƴan uwansu.
Sun kuma nuna farin ciki da ƙoƙarin babban daraktan ayyuka na musamman AVM Ibrahim Umaru mai murabus domin shine wanda ya tsaya tsayin daka wajen ganin Gwamnatin kano ta taimaka musu da irin wannan tagomashi
Haka kuma tallafin da aka basu sun hada da Naira dubu dari biyar sai manyan buhunan shinkafa guda uku, da katan na taliya guda uku da buhunan gero 3 ga iyalan marigayi Laftanar Kanal AH Ali, yayin da iyalan sauran sojoji uku suka karbi Naira dubu ɗari biyu, da manyan buhunan shinkafa 2 da katan na taliya 2, da buhunan gero guda biyu kowanne.
You must be logged in to post a comment Login