Labarai
Gwamnatin kano ta dawowa da al’ummar garin Riruwai makaranta da wani kamfani ya mayar da ita ofishin sa

Gwamnatin jihar kano ta dawowa da al’ummar garin Riruwai dake ƙaramar hukumar Doguwa wata makaranta mallakin gwamnati da wani kanfanin haƙar ma’adanai ya mayar da ita ofishin sa, tare da samar da dai-dai to tsakanin al’ummar yankin bisa wani saɓani da ya kunno kai a yankin dalilin haƙar ma’adanai tsakanin wasu ɓangarori a yankin
Kwamishina ma’adanai da albarkatun ƙasa Alhaji Hamza Safiyanu kachako ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki dake yankin na Riruwai domin samar da dai-dai to zakanin al’ummar garin da sauran kanfanoni masu aikin ma’adanai a yankin.
Hamza safiyanu kachako ya ce wannan dambarwa da ta kunnu kai tsakanin bangarorin guda biyu yanzu haka gwamnati ta shiga tsakani kuma an samar da dai-dai to.
Haka zalika Kwamishinan ya umurci wannan kanfanin da ya tare a cikin makarantar da ya gaggauta barin cikin makarantar domin al’ummar yankin su ci gaba da karatu a cikin makarantar.
Da yake ƙarin haske shugaban ƙaramar hukumar Doguwa Alhaji Abdulrashid Rilwan ya ce wannan abu da ya faru jarrabawa ce kuma an samu daidai tsakanin al’ummar yankin.
A nasa jawabin ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki na yankin Riruwai Malan Usman Sule Riruwai yace wannan zama da akayi yasa an fahimci juna domin samarwa da garin nasu ci gaba
Taron dai ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki dake yankin yayin da a karshe suka amince da yin aiki tare ta yadda za a warware duk wasu matsalolin da suka taso daga yarjejeniyar ci gaban al’umma da aka kulla da kamfanin hakar ma’adanai a yankin.
You must be logged in to post a comment Login