Connect with us

Labarai

Hatsarin mota ya rutsa da wasu dalibai 23 a garin Dandunduru dake karamar hukumar Gaya

Published

on

Hatsarin mota ya rutsa da wasu dalibai 23 da malamansu da suka taso daga karamar hukumar Misau ta Jahar Bauchi zuwa nan Jahar Kano a garin Dandunduru yankin karamar hukumar Gaya da misalin karfe 11:00 na safiyar Talatar nan.

Wani magidanci wanda hadarin ya faru akan idonsa mai suna Ibrahim Adamu ya ce hadarin ya faru ne sakamakon taho mugama da wata mota inda daliban maza 13 da kuma mata 10 suka rasu.

Ibrahim Adamu ya kuma bayyana cewa direbobin motocin biyu suna yin gudu na wuce sa’a ne wanda hakan ne ya haddasa aukuwar mummunan hadarin, inda aka kwashe wadanda suka jikkata aka kai su babban Asibitin garin gaya domin duba lafiyarsu sakamakon munanan raunuka da suka samu .

Jami’in hudda da jamaa na rundunar Yansanda ta Jahar Kano DSP Magaji Musa Majiya inda ya tabbatar da faruwar hadarin inda yace ana nan ana kwashe gawawwakin.

DSP Magaji Musa Majiya ya ce rundunar ‘yan sandan na nan tana kokarin yin abinda ya kamata kan hadari.

Kakakin hukumar kare aukuwar hadurra ta kasa FRSC shiyyar Kano, Kabiru Ibrahim Daura ya bayyana cewa, bayan rasuwar daliban 23 , wasu mutum 3 sun samu raunuka inda yanzu haka mutum 2 ke babban asibitin karamar hukumar Gaya yayin da aka kawo mutum 1 wani asibiti a nan cikin garin kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!