Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hisbah ta cafke matashi kan yunkurin haikewa budurwar abokinsa

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta bayyana cewa, jami’anta sun samu nasarar kame wani matashi da ake zargi da yunkurin haikewa budurwar aminisa.

Jami’an na Hisba dai sun kama shi ne lokacin da ya gayyaci buduruwar zuwa sabon gidan da ya gina, inda ake zargin ya kai ta gidan ne da nufin aikata badala.

Rahotonni sun bayyana cewa, wanda aka kama din shi ne babban abokin saurayin budurwar kuma shi ne yake raka shi zance, inda ya rage lokaci kadan a daura musu aure.

Matashin dai ya bayyana wa Freedom Radio cewa ya gayyaci budurwar ne domin ta ga sabon gidan da ya gina, amma babu abun da ya shiga tsakanin sa da ita.

Malam Bukari Mika’il shi ne mukaddashin kwamandan Hisba mai kula da ayyuka na musamman ya shaida wa Freedom Radio cewa hukumar ba zata zuba ido akan irin wadannan lamura na aikata badala ba.

Rubutu masu alaka:

Hisbah ta cafke masu Kanjamau

Yadda hukumar Hisbah ta sauke ‘yan kwamitin gudanarwarta

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!