Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB ta ce sama da dalibai miliyan biyu ne zasu rubuta jarabawa

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa wato JAMB, ta ce; sama da dalibai miliyan biyu ne ake saran za su rubuta jarabawar ta JAMB a wannan shekara.

 

Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka ga manema labarai a garin Ilorin babban birnin jihar Kwara.

 

Ya ce, a shekarar 2017 hukumar ta samu ribar naira biliyan goma sha biyu wadanda kudade ne da ta tattara a wajen dalibai da ke rubuta jarabawar ta JAMB, yana mai cewar, kuma tuni suka sanya naira biliyan bakwai da miliyan dari takwas a asusun tarayya.

 

Shugaban hukumar ta JAMB ya kuma ce hukumar ta bullo da sabbin dabaru na zamani wadanda za su taimaka wajen inganta ayyukan hukumar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!