Connect with us

Labaran Kano

Hukumar tace fina-finai ta kasa ta kone fina-finan batsa a Kano

Published

on

Hukumar tace fina-finai ta kasa ta yi kira da ‘yan kasuwa da kamfanonin shirya fina finai dasu mai da hankali wajen inganta harkokin saida fina finai masu mahimmanci da ma’ana a cikin alumma.

Shugaban hukumar  mai kula da shiyyar Kano Alhaji Umar Fagge ne ya bayyana haka lokacin da  suke kona fina-finai na basa a harabar hukumar dake nan kano.

Ya kara da cewa sun kama fina-finai batsa guda dubu biyar a kasuwanin jihar nan domin karkabe bata gari a cikin kasuwanin.

A nasa jawabin hakimin karamar hukumar  Dala Alhaji Abdullahi Lamido Sunusi Turakin Kano ya ce, dole ne iyayen yara su sa ido sosai a irin fina- finai da yaransu suke kallo domin wasu fina-finai suna bata tarbiyar yara.

Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa shuwagabannin kamfanonin shirya fina-finai da mayan jami’an tsaro sun hallaci kona fina -finai na basa guda dubu biyar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!