Labarai
Ina zargin Gwamna Ganduje da Kwamishinan Ƴan sandan Kano da cin zarafina – Inji Muhyi Magaji
Tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce, yana zargin gwamna Ganduje da Kwamishinan Ƴan sandan Kano da cin zarafinsa.
Rimin Gado ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio, kwana guda bayan da jami’an ƴan sanda suka kai sumamen kama shi a gidansa.
“A baya ma mun shirya taron ranar yaƙi da cin hanci da rashawa suka zo suka tarwatsa mu, ba mu ce komai ba, duk abubuwan da ake mana da sanin ofis ɗin su ake mana”.
“Sun zo sun zarge ni da almundahana an yi bincike ba a same ni da laifi ba, sun takura dole dole sai an caje ni da ƙarya, kuma yanayin hakan ne don ya farantawa wasu ba don sanin aikin sa ba” a cewar Muhyi.
“Bayan sallar magriba ina tare ba baƙi, kawai sai na ji ana dirgowa gidana ko da na bincika sai aka ce wai gwamna ne ya aiko a kama ni, ban san me nayi ba, sai na ce Zahraddeen ya ɗauki mota ya fita ya gano mana ko su wanene, amma sai suka riƙa cewa wai sun zo ne su bani takardar gayyata, amma da na gano so suke in na fito su kamani sai na ƙyale su” a cewarsa
Muhyi Magaji ya kuma ce “An zo gaɓar da bai kamata na bar su ba a matsayina na ɗan ƙasa, tun ya keɓanta abin, bana iya shiga harkokin jama’a saboda fargaba amma sai nake zama a gida, hakan ma ba sa son gani”.
Dakataccen shugaban ya ƙara da cewa lokaci yayi da zai nuna ƴancin da yake da shi a matsayin sa na ɗan ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login