Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Iyayen Yaran da dan hidimar kasa ya kashe ,sun nemi ayi musu adalci.

Published

on

Iyayan yaran nan dan shekaru 7 da ya fito daga karamar hukumar Bebeji sun bukaci ayi adalci sakamakon zargin da aka yiwa wani dan yiwa kasa hidima mai suna Jepthan Peter Makwin da kashe dan nasu.

Mahaifiyar yaran mai suna Zainab Abubakar Suleiman ta zargi Mr Mawkin da dalilin kashe mata da, inda tace ba zata taba yafe masa ba.

Mahaifin yaran mai suna Suleiman Aliyu ya shaidawa ‘’yan jarida cewa marigayi dan sa Hassan suna zuwa masaukin ‘’yan bautar kasar ne domin su tsinki itace na burtu.

 

Yace dalilin haka ne yasa ‘’yan yiwa kasa hidimar suke kaunar wadannan kananan yara har suke raba musu itaciyar bishiyar ta burtu .

Yace bayan raba musu ne dan nasa ya koma domin karbar itaciyar bishiyar wanda hakan ta sa dan bautar kasar ya fusata.

Malam Aliyu yace dan bautar kasar ya daki yaron nasa ya hada kansa da bango sau shurin masaki inda yace sun ki su dauki doka a hannunsu domin suna da yakini cewa Gwamnati zata tabbatar da adalci.

Wani mazaunin garin na Bebeji da ya dauki marigayi Alhassan Muhammad Rabiu zuwa asibiti yace marigayi Hassan ya rasa ransa ne bayan an kaishi asibiti

A nasa bangaren jamiin hulda da jamaa na rundunar Yansandan ta jahar Kano DSP Abdullahi Haruna yace matsalar a yanzu tana banagaren bincike na rundunar yansanda ta jahar Kano wato CID

Da yake mayar da martani shugaban masu yiwa kasa hidima na jahar Kano Ladan Baba yace ba mai yiwa kasa hidimar ba ne yayi sanadin mutuwar yaran ba.

A sanarwar da ya fitar wa da manema labarai Ladan Baba yace Mr Mawkin ya dai bi yaran ne har ya fadi sannan haka yayi sanadin mutuwar sa.

A nasa bangaren Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje shi da shugaban karamar hukumar Bebeji sun ziyarci iyalan marigayi Hassan inda suka jajantawa mahaifin yaran Suleiman Aliyu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!