Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’ar Yusuf Maitama Sule za ta kashe sama da naira biliyan uku

Published

on

Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke nan Kano ta ce za ta kashe sama da naira biliyan Uku wajen kafa sabuwar tsangayar aikin likitanci a jami’ar.

Shugaban jami’ar ta Yusuf Maitama Sule farfesa Mustapha Ahmed Isah ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala kare kunshin kasafin kudin jami’ar a gaban kwamitin kula da harkokin ilimi mai zurfi na majalisar dokokin jihar Kano a yau.

Ya ce jami’ar za ta kuma karasa aikin gina wasu dakunan kwanan dalibai guda biyu.

A nata bangaren kwamishiniyar ilimi mai zurfi na jihar Kano Dr. Mariya Mahmud Bunkure ta ce maaikatar za ta mai da hankali wajen kula da bada tallafin karo karatu ga ‘yan asalin jihar a shekara mai zuwa.

A wani labarin kuma hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta ce har yanzu tana kan bakarta wajen tabbatar da cewa dukkannin manyan bincike-bincike na zargin cin hanci da rashawa da hukumar ke gudanarwa.

 

Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa  shugaban kwamitin kula da ilimi mai zurfi Ali Ibrahim Isah Shanono na cewa majalisar za ta tsefe kunshin kasafin kudin domin tabbatar da cewa ta dace da bukatun al’ummar jihar Kano.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!