Labarai
Jam’iyyar ADC ta zargi EFCC da zama ƴar koren APC

Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta zargi hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da cewa ta zama ƴar koren jam’iyya mai mulki ta APC, inda suke zaɓar waɗanda suke yin bincike a kansu.
Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta hannun sakataren yaɗa labaranta, Malam Bolaji Abdullahi, ta ce abin da EFCC ke yi a yanzu na sake buɗe shari’o’i da aka kammala da fito da fayil-fayil na shekaru da suka wuce har ma da matsa wa mambobin jam’iyyar, ba irin aikin da aka san hukumar ba ce da shi, illa wadda ke yi wa wani aiki.
A baya-bayan nan dai mambobin jam’iyyar haɗakar sun ce sun samu sakonnin gayyata daga EFCC waɗanda suka ce suna alaƙa da siyasa.
Don haka ne ADC ta yi kira ga dukkan ƴan Najeriya, ƙungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu da su yi watsi da irin abin da hukumar ke yi na kama ƙarya don cimma manufofinta.
You must be logged in to post a comment Login