Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jihar Taraba: Yan bindiga dadi sunyi ajalin akalla mutane uku tare da jikkata wasu bakwai

Published

on

Akalla makiyaya uku ne suka mutu wasu bakwai kuma suka jikkata bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta a kasuwar dabbobi dake Mararrabar Kunini a karamar hukumar Lau a Jihar Taraba.

Wani jam’in ‘dan sanda da aka sakaya sunansa ya shaidawa manema labarai cewa da yammacin jiya Lahadi cewa ‘yan bindigar sun arce bayan kai harin, kuma ana ci gaba da nemansu ruwa a jallo.

Rundunar ‘yan-sandan Jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta-bakin mataimakin Sufurtandan ‘yan sanda David Misal, kuma ba su kai ga kama ko da mutum guda game da harin ba, amma duk sun tsaurara matakan tsaro a yankin don kuacewa sake aukuwar hakan.

Wani daga cikin ‘yan kasuwar Malam Kawu ya ce suna tsaka da hada-hadar cinikayyar Shanu da Awaki da kuma Tumaki sai suka ji harbe-harbe wanda daga nan ne suka fara gudun tsira.

Shi ma wani mai sayar da kayan sawa na gwanjo Mista Josiah Bante ya ce maharani ba su komai ba a kasuwar, in banda harbin mutane da suka rika yi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!