Labarai
Kafar sadarwar X za ta taimaka wajen Tallata ayyukan gwamnatin Kano – Waiya

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya kaddamar da kungiyar masu tallata aiyukan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a Ƙafar X
Yayin da yake kaddamar da su a yau Talata 11/2/2025, Waiya ya bayyana gamsuwar sa da yadda tsarin kungiyar yake. Inda yace gwamnan Kano yana ayyuka da dama domin ciyar da jihar Kano gaba, amma ba a yada aiyukan yadda ya kamata.
Wanda hakan yasa aka bijiro da tsarin da zai yaɗa ayyukan gwamnatin Jihar Kano a dukkanin kafafen sada zumunta.
Ya kuma bukaci ya’yan kungiyar da su yi amfani da shafin na X wajen tallata ayyukan alkhairin da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake yiwa kanawa, tare da kaucewa yaɗa labaran da suke bana gaskiya ba.
Da yake jawabi Shugaban Kungiyar Mukhtar Aliyu Sadiq ya bayyana Jin dadin sa kan yadda Kwamishinan Yaɗa Labarai ya jawo su cikin tsarin tallata ayyukan Gwamnatin Jihar ta Kano.
Inda yayi alkawarin tabbatar da yaɗa labaran Gwamnatin Jihar Kano ta hanyar data dace ba tare da cin zarafi koh kyama ga ko wani banagare ba.
You must be logged in to post a comment Login