Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai-tsaye : lauyoyi na musayar yawu a Kaduna

Published

on

11:12

An fara gudanar a da shari’ar daukaka karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya shigar gaban kotun daukaka kara dake zama a jihar Kaduna.

Sai dai kafin fara saurarn karar lauyoyin bangarorin biyu suna ta musayar yawu kan yadda za’a saurari karar.

Wakilin mu Bashir Muhammad Inuwa da yake cikin kotun ya rawaito cewar lauyan masu gabatar na bangarori biyu ne ke fafatawa.

Kotun daukaka kara dake zamanta a kaduna karkashin alkalai 5 ta  sanya yau Litinin18 ga wannan watan na Nuwamba don saurarn karar da Jam iyyar PDP da dan takarar gwamna Abba kabir Yusuf suka shigar ya shigar gabanta.

A halin yanzu kotun daukaka kara dake jihar Kaduna ta shirya don fara sauraran daukak karar  da dan takarar gwamnan na jam’iyyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya shigar gaban ta yana kalubalantar hukunkunci da mai shari’a Halima Shamaki ta zaratar a watan jiya na Okotoba.

Mai shari’a Halima Shamaki tayi watsi da karar tana mai cewar, karar bata da cikakkun hujoji

Sai  dai kawo yanzu an dan sami sabani a tsakanin bangarorin biyu kafin fara sauraran karar.

Wakilin mu na Kotu Bashir Mohammad Inuwa ya rawaito cewar tun daga misalin karfi  da rabi na safe harabar kotun ya fara daukar harami.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!