Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai tsaye: Muktar Ishaq Yakasai ne na karshe -Sunayen Kwamishinoni

Published

on

Muktar Ishaq Yakasai ne na karshe cikin jerin sunayen da aka tantance a majalisar dokoki ta jihar Kano.

Bayan da shugaban majalisa ya kira sunan Muktar Ishaq Yakasai sai shewa ta karade zauren majalisar har sai da shugaban majalisar ya nemi kowa ya zauna a kammala tantancewar.

wasu daga cikin ‘yan majalisar dai sun tamabaye irin gudunmawar da Muktar Ishaq Yakasai ya bayar a yayin da yake rike da shugaban karamar hukumar Birne da Kewaye.

An kammala tantance Kabiru Ado Lakwaya wanda aka yi masa tambaya kan yadda yayi gwagwarmaya a rayuwa.

Kazlika shugaban majalisa Abdul’aziz Garba Kafasa yayi masa tambaya idan aka nada shi kwamishinan wasanni wanne irin cigaba zai kawo.

Kabiru Ado Lakwaya ya amsa da cewar babu guda ba ja da baya zai bunkasa harkokin wasanni a jihar Kano.

Yayin da ake tantance shugaban kwamitin sake yin nazari kan karantun Almajiranci da na tsangayu Baba Impossible, yace lokacin da yake rike da mukamin shugaban hukumar ilimi mai zurfi ya kawo sauye-sauye.

A cewar, Babba Impossible ya rike ma’aikatar ne na watanni hudu kuma yayi kokarin ganin an biya kudin tallafin karatu na dalibai na cikin gida da na ketare.

An dai tantance Shehu Na’Allah Kura wanda wasu daga cikin ‘yan majalisar suka yi masa tambayoyi  kan yadda ya gudanar da aikin sa yana kwamshinan kasafin kudi da tsare-tsare.

Shehu Na’Allah Kura ya bayyana cewar, ya gaggauta aiwatar da kasafin kudin bara kan lokaci.

Bayan da aka tantance tsohun kwamishinan shari’a sai kuma tsohun kwamishinan lafiya Dr, Kabiru Ibrahim Getso wanda yake amsa tambayoyin ‘yan majalisar.

Dr, Kabiru Ibrahim Getso dai ya fara da amsa tambayar irin cigaban da ya kawo a gwamnatin Ganduje a wa’adin sa na farko.

wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewar, Kabiru Ibrahim Getso na cewa ya kawo cigaba da suka hada da nada linkafar wasu jami’an kiwon lafiya da samar da sabbin asibitoci da dai sauran su.

A halin da ake cikin ana tsaka da tantance tsohun kwamishinan shari’a Barrister Ibrahim Muktar yayin da ya bayyana irin cigaban da ya kawo a zangon farko na gwamnatin Ganduje.

An dai kammala tantance tsohuwar mataimakiyar kwamandan Hisbah Dr, Zara’u Muhammad Umar.

Kawo yanzu Sadiq Wali aka kamala tantancewa yayin da aka yi masa tambayoyi.

A halin da ake cikin shugaban majalisar dokoki ya kira Muhammad Sunusi Kiru yayin da fara bayanai kan rauywar sa.

Muhammad Sunusi Kiru dai yayi aiki a ma’aikatar Wasanni ta kasa.

Kuma dan majalisa Sale Ahmed Marke daga mazabar Dawakin Tofa ke masa tamabayoyi.

Kunshin sunayen da gwamnan ya aikewa majalisar dokoki sun hada da:

Engr. Muazu Magaji

Barrister Ibrahim Muktar

Musa Iliyasu Kwankwaso

Dr. Kabiru Ibrahim Getso

Mohammed Garba

Nura Mohammed Dakadai

Shehu Na’Allah kura

Dr. Mohammed Tahir

Dr. Zahara’u Umar

Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa

Sadiq Aminu Wali

Mohammed Bappa Takai

Kabiru Ado Lakwaya

Dr. Mariya Mahmoud Bunkure

Ibrahim Ahmed Karaye

Muktar Ishaq Yakasai

Mahmoud Muhammad

Muhammad Sunusi Saidu

Barrister Lawan Abdullahi Musa

A halin yanzu dai ana tsaka da tantance Ibrahim Ahamed Karaye yayin da aka fara tambayar sa da cea ko ya taba rike mukamin kwamishina.

Wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewa, akasarin tambayoyin da ake wadanda ake tantancewar bai wuce ko sun rike mukamai ba da kuma yadda suke gudanar da ayyukan su.

Shugaban majalisar Abdu’aziz Garba Gafasa na dai tantancewar ne da harshen turanci yayin da kuma wasu ‘yan majalisar ke yi musu tambayoyi da harshen Hausa.

Bayan da majalisar ta zauna da misalin karfe tara da minti Arba’in da biyar 45, shugaban majalisar Abdul’azizi Garba Gafasa ya fara kiran sunayen da gwmanan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike musu.

An dai fara da Musa Iliyasu Kwankwaso sai Muhammad Garba sai kuma Murtala Sule Garo.

Harabar majalisar dokoki ta jihar Kano ta dauki harabi biyo bayan sunayen da gwamnatin Kano ta aikewa majalisar a jiya.

Da safiyar yau Talata ne wakilin mu na majalisar dokoki ta jihar Kano Abdullahi Isa ya rawaito cewar an dauke matakan tsaro a ciki da wajen harabar majalisar.

Wakilin na mu ya kara da cewar wadanda aka aike da sunayen na su tuni wasu suka isa harabar majalisar yayin da kuma wasu  ke shiga  cikin majalisar a halin yanzu.

Ana sa ran nan gaba kadan ne majalisar dokoki ta jihar Kano zata fara zaman tantance kunshin sunayen da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa majalisar a jiya litinin.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!