Labarai
Kano: INEC ta haramtawa ‘yan bautar kasa aikin zabe
Hukumar zabe mai zamankanta ta kasa INEC ta ce babu wani dan bautar kasa da zata tura karamar Hukumar Bebeji domin gudanar da aikin zaben cike gurbi da za’a gudanar a ranar 25 ga watan da muke ciki saboda dalilai na tsaro.
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano Farfesa Riskuwa Arabi Shehu ne ya bayyana hakan a wani taron Manema labarai dake gudana yanzu haka a dakin taro na hukumar zabe dake nan Kano.
Farfesa Riskuwa Arabi shehu ya kara da cewa INEC ta dauki ma’aikata ‘yan bautar kasa na jami’ar Bayero ta Kano kimanin su dubu uku da dari hudu da hamsin da shida ta horas dasu kan yadda zasu gudanarda aikin zaben cike gurbi a kananan hukumomin da za’a sake gudanarda zaben cike gurbi jihar Kano.
Shugaban Hukumar Riskuwa Arabi Shehu ya kuma nanata cewa zasu gudanar da zaben cike gurbi cikin gaskiya da adalci domin ganin an yiwa kowacce jam’iyya adalci.
Farfesa Riskuwa Arabi Shehu ya ce daga yanzu har zuwa kowane lokaci hukumar zabe ta jihar Kano INEC tana saran zuwan kayayyakin aikin zaben daga Babban bankin kasa CBN, kuma za su tabbatar an tura kayayyakin zaben zuwa kananan hukumomin jihar Kano akan lokaci.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano INEC na cewa zata samar da ingantaccen yanayi mai kyau domin ganin an gudanar da zaben cike gurbi cikin kwanciyar hankali da lumana.