Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano na kan gaba -WAEC

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar WAEC ta sanya jihar Kano a cikin jerin jihohi biyar 5 da suka fi yin kwazo a jarrabawar hukumar da aka yi a bana.

Mataimakin magatakardar hukumar Mr, Henny Adewumi ya sanar da hakan a yayin taron kwamtin jiha wanda aka yi a harabar hukumar KERD dake nan Kano

Sauran jihohin sune Abia da Lagos da Bayelsa da kuma Nassarawa.

Haka zalika rahotanni sun bayyana cewar Mr Adewumi yace wadannan jihohin daliban da suka zauna rubuta jarrabawar sun sami nasarar samun Kiredit a darusan Lissafi da Ingilishi

Mataimakin magatakardar hukumar ta WAEC ya gargadi dalibai da su guji zuwa cibiyoyin rubuta jarrabawar da ake satar jarrabawar, wanda akasarin wasu makarantun ke amfani da su wajen karbar kudade daga dalibai wadanda suke son cin jarrabawa ba tare da sun zauna rubuta WAEC din ba..

Ya kuma bukaci shugabanin makarantun da su dinga taimakawa masu bukata ta mussaman wajen cike takardun form na yin jarrabawar.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!