Connect with us

Labaran Kano

Kano: Yan sanda sun kama wani da ake zargin dan Boko Haram

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa, ta kama wani da ake zargin dan kungiyar Boko Haram ne bayan daya gudo daga garin Maiduguri zuwa nan Kano kuma yake yin basaja a matsayin mahaukaci yana yawon neman sadaka, a unguwar Mandawari dake cikin birnin Kano.

Mutumin wanda har kawo yanzu rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana sunan sa ba, rahotonni sun bayyana cewa ya dade yana yawo a unguwannin yankin yana neman sadaka.

A cewar Rundunar ‘yan sandan, wani soja ne da ke aiki a garin na Maiduguri ya dawo gida hutu inda ya ga mtumin a unguwarsu ta Mandawari nan take ya shaida shi inda ya sanar da jami’an ‘yan sanda kuma ana kama shi.

Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmad Iliyasu ya bada umarnin mika shi shalkwatar rundunar da ke unguwar Bompai domin fadada bincike.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,282 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!