Connect with us

Labaran Kano

Karfafawa matasa gwiwa zai bunkasa al’umma- Dan masanin Kano

Published

on

Dan masanin Kano Alhaji Abdullakadir Yusuf Maitama Sule ya ja hankalin matasa dasu tashi su nemi na kansu su, su daina dogara da gwamnati.

Alhaji Abdullakadir ya bayyana haka ne lokacin da yake bude sabon ofishin sayar da kayan gine-gine dake kan titin Lodge Road.

Ya kara da cewa dole ne matasa su tashi su nemi na kansu a rayuwar su  haka kuma matasa sun fi maida hankali wajen shaye-shaye a wannan lokaci ga sana’oin iri daban-daban kamar su takalmi dinki da dai sauran su.

Yace wannan ofishi da wannan matashi ya bude abune mai mahimmanci a rayuwar matasa.

Shi ma wannan ya bude ofishin sayar da kayan gine-gine Injiniya Khalifa Rabi’u yace yayi wannan kokari ne domin taimakawa kan sa da kuma sauran mutane da suke son koyan sana’oin dabam dabam.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa matasan suna kira da gwamnati data cigaba da basu hadin kai wajen bunkasa sana’oin masu inganci a rayuwarsu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!