Labarai
Kayan masarufi sun karye, Naira ta yi daraja a Nigeriya
Rahotanni na nuna cewa a karon farko Najeriya tun bayan da aka fara samun karyewar Naira da kuma hauhawan farashi, Naira ta samu daraja tare kuma da samun karyewar farashin kayayyaki kusan da kaso hamsin ko sama da haka a kasar nan.
Wannan sauyi dai an sameshi ne biyo bayan karancin kudin da aka samu a kasar, sanadiyar sauyin da babban bankin kasar nan yayi na naira 200 da 500 da 1000.
Sai dai masana a fannin tattalin arziki irin su Abdussalam Kani na kwalejin ilimi ta Sa’adatu rimi dake Jihar Kano cewa ‘darajar da Naira ta samu a kasar nan, an samu ne sakamakon karancin kudin da aka samu a kasar, bankuna sun tsaya cak, CBN sun buga kadan, bankuna sun boye, wanda idan komai ya dai-daita zata koma yadda take.’.
”Wannan matsalar ta haifarwa kasuwanci durkushewa, masu kanana da matsakaitar sana’o’i sun gaza wajen biyan basussukan banki, sana’o’i duk sun tsaya cak.”
Abdussalam Kani ya kara da cewa ‘ suma kayan masarufi sun karye ne saboda ba kudi a hannun al’umma, wanda ya tilastawa masu kayan karya kayansu, don a samu a siya.
Sai dai kuma a hannu guda yace ”yayin da komai ya dai-daita, Nairar zata ci gaba da karyewa, shi kuma kayan masarufin zasu cigaba da hauhawa.”
Dr Kani ya ce ”Idan har anaso kudin kasar nan suyi daraja sai kasar ta fara fitar da kaya kasashen waje, sannan kayan da ake shigowa dasu kasar basu kai wadanda ake fitar wa waje ba, wannan ne kadai zaisa kasar ta samu kudaden kasashen wajen, wanda kuma shi zai sa darajar Naira ta daga.”
Rahoton:Shamsiyya Farouk Bello
You must be logged in to post a comment Login