Connect with us

Labarai

Kotu ta yanke hukuncin biyan diyyar miliyan 10 ga babban hafsan soji Tukur Buratai ga mutum 11yan jihar Gombe

Published

on

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci tare da umartar babban hafsan sojin kasan Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai da ya biya wasu mutane goma sha daya ‘yan asalin jihar Gombe diyyar naira miliyan goma sha daya sakamakon tsare su ba bisa ka’ida ba da sojoji su ka yi.

Da take yanke hukuncin, alkalin kotun mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayyana cewa kamawa da kuma tsarewar da sojoji suka yi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan.

Wadanda sojojin suka kama suka tsare a ranar shida ga watan Yuli sun hada da: ’’James Yusuf da Ishaya Ali Poshiya da Nehemiah Yohanna Poshiya Da Hosseini Poshiya da Hamma Poshiya da Yusuf mafindi da Yila Boyi da James Bare da Ezekiel Dandaudu da Ali Ishaku da kuma Ilya Bala.

Haka zalika kotun ta kuma bukaci sojojin da su gaggauta sakin mutanen sannan a biya kowane guda daga cikin su diyyar naira miliyan dai-dai.

Tun farko dai bayanai sun ce sojojin sun kama mutanen goma sha daya ne sakamakon zargin su da ake yi da kisan wani mutum mai suna David jauro Stephen a gonar sa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,610 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!