Labarai
Kotun Koli tayi watsi da karar Atiku
Yau Laraba Kotun Koli ta fara sauraron daukaka karar da Atiku Abubakar ya shigar a gabanta, yayin da yake kalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a babban zaben da aka yi a wannan shekara ta 2019.
Sai dai Kotun koli ta yi watsi da karar tun kafin aje ko’ina da jam’iyyar PDP da dan takarar ta, Atiku Abubakar suka shigar suna kalubalantar nasarar da aka bayyana abokin takararsa, Muhammadu Buhari ya yi a zaben da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara.
Alkalin Alkalan babbar kotun Najeriya, mai shari’a Tanko Muhammad da ya jagoranci alkalan babbar kotun su shida ya sanar da hukunci kan shari’ar cikin sadarori uku da suka kawo karshen duk wata takaddama kan wancan zabe.
Atiku ya musanta ikrarin jami’yyar APC cewa bai cancanci tsayawa takara ba
Zamfara:rundunar yan sanda ta musanta rahotannin kai hari ga shaidun Atiku Abubakar
Atiku:ya nemi kotu ta ayyana shi ya lashe zabe
Babban Alkalin Alkalan na kasa ya bayyana cewa sai a nan gaba za a bayyana dalilan da ya sanya alkalan suka yanke wannan hukunci.
Ya kara da cewa makonni biyu suka yi shi da sauran alkalan suna karanta dukkan bayanai da kuma shaidun da aka gabatar kan karar, inda suka lura da rashin madogara a karar.
An yanke wannan hukunci da dukkan Alkalan su shida suka amince da shi cikin abin da bai kai Awa guda ba, bayan da kotun ta saurari bayanan daukaka kara daga bakin mai gabatar da kara.