Kasuwanci
Ku ci gaba da riƙe martabar mu ta kasuwanci a Kano – Sarkin Kano ga ƴan kasuwa
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya buƙaci ƴan kasuwa da su ci gaba da riƙe martabar jihar ta fannin kasuwanci da ta shahara a kansa.
Sarkin ya buƙaci hakan a wajen taron bikin cikar ƙungiyar masu kamfanonin jiragen sama ta ƙasa shekaru Arba’in da shida da kafuwa.
Alhaji Aminu Ado Bayero wanda Ɗan Amar ɗin Kano Alhaji Aliyu Harazimi Umar ya wakilta a wajen taron.
“Jihar Kano ta shahara a faggen kasuwanci a fadin Ƙasar nan har ma Da Ƙasashen Afrika ta Yamma, wannan zai ci gaba da ɗorewa ne matuƙar ƴan kasuwa suka riƙe martabar kasuwanci”.
Ya ci gaba da cewa “Masarautar Kano za ta ci gaba da hada kai da ƙungiyar masu kamfanonin jiragen sama don ciyar da fannin gaba da kuma bunƙasa tattalin arziƙi”.
A nata ɓangaren shugabar ƙungiyar Madam Susan Akporiaye ta ce, sun zaɓi Jihar Kano ne domin muhimmacin da ta ke da shi a fannin kasuwanci tun zamanin baya.
Wakilin Freedom Radio Shamsu Da’u Abdullahi ya ruwaito cewa, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya haɗawa tawagar ƙungiyar ƙwaryaƙwaryar hawan Daba a harabar masarautar ta Kano.
You must be logged in to post a comment Login