Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ku murkushe masu fafutukan neman raba Najeriya – martanin IGP ga ƴan sanda.

Published

on

Mai riƙon muƙamin sufeto janar na ‘yan sandan ƙasar nan Usman Alkali ya bai wa jami’an ‘yan sanda umarnin murkushe duk wasu masu yunƙurin ɓallewa daga kasar nan.

 

Usman Alkali ya buƙaci ‘yan sandan da su yi amfani da iƙon da suke da shi don tabbatar da cewa sun hukunta masu neman tada zaune tsaye ko kuwa a wani yanki su ke a ƙasar nan.

 

Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda a baya-bayan nan ake kashe ‘yan sanda a yankunan kudu maso kudu da kuma kudu maso gabashi, yana mai umartar ‘yan sandan da su kare kansu daga ‘yan ta’adda.

 

Mai riƙon mukamin sufeta janar na ‘yan sandan ya bayyana hakan ne a garin Enugu lokacin da ya ke ƙaddamar da wani atisayen ‘yan sanda mai taken Operation Restore Peace a dandalin Micheal Okpara da ke Enugu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!