Kiwon Lafiya
Kungiyar kwadago: ba zata amince da kasa da dubu talatin ba a matsayin karanci albashi
Shugabancin kungiyar kwadago ta kasa bangaren Joe Ajaero, ta ce, gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar nan ba zasu sanya hannu kan duk wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya ba game da mafi karancin albashi da ya gaza naira dubu talatin.
Shugaban bangaren kungiyar kwadagon ta United Labour Congress Joe Ajaero ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Lagos.
Ya ce, dubu ashirin da hudu ba zai taba kasancewa mafi karancin albashi ba, a don haka ya kamata gwamnati ta sake tunani kan batun.
Ya kuma ce kwamitocin nazarin mafi karancin albashi da suka kammala aikin su a baya-bayan nan, sun amince kan cewa naira dubu talatin ta kasance mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan.
Shugaban kungiyar ta United Labour Congress ya nanata cewa ‘yan kwadago a kasar nan ba za su taba amincewa da dubu ashirin da hudu da wakilan gwamnati suka sanar ba