Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar Dattawa za ta gudanar da bincike kan zargin karbar kudaden alhazai ba bisa ka’ida ba

Published

on

Majalisar Dattawa ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin karbar wasu kudade ba bisa ka’ida ba daga hannun alhazai da suka gudanar da aikin Hajjin da ya gabata.

Shugaban kwamitin karta-kwana kan samar da masaukai da ciyar da alhazai na majalisar Dattawa Sanata Adamu Aliero ne ya bayyana hakan, yayin wani taron jin ra’ayin jama’a game da aikin Hajjin da ya gabata wanda aka gudanar jiya a Abuja.

Ya ce akwai rahotannin karbar kudade ba bisa ka’ida ba da kuma coge wajen ciyar da alhazai abinci da samar musu da masaukai marasa kyau da kuma matsaloli da suka shafi zirga-zirgar su a kasa mai tsarki.

Sanata Adamu Aliero ya kuma ce bayanai da ke hannunsu yanzu sun nuna cewa an damfari alhazai wajen karbar kudade ba bisa ka’ida ba da kuma kara farashin kudin aikin Hajji da gangan da dai sauran laifuka da dama.

A cewar sa akwai bayanai da suka nuna cewa alhazan kasar nan ne suka biya kudin aikin hajji mafi tsada a nahiyar afurka kuma suna daya daga cikin alhazan da suka biya kudin aikin hajji mafi tsada a duniya.

Akalla dai alhazan kasar nan dubu tamanin da daya ne suka sauke farali a shekarar da ta wuce, yayin da a bana ake tsammanin maniyyata dubu casa’in da biyar ne za su sauke farali

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!