Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar sarakuna : Ganduje ya bada umarnin da a gyara gidan Shattima

Published

on

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa Kwamishinan ayyuka da cigaba Injiniya Mu’azu Magaji umarnin da a gyara gidan tarihi na Shattima a matsayin ofishin majalisar masarautun gargajiya ta jihar Kano, duk da umarnin kotu na  dakatar da sabuwar dokar majalisar masarautar Kano.

Gidan Shattima dai na kusa da fadar maimartaba sarkin Kano  Muhammadu Sunusi na II.

Wannan nakunshe cikin sanarwar da sakataren yada labaran gwamna Abba Anwar ya fitar cewa  gwamnan ya yanke shawarar yin hakan a wani matakin na shirye-shiryen kaddamar da sabuwar majalisar masarautar Kano.

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Ganduje da Sarkin Kano sun gana da masu zuba jari daga kasar China

Ina rokon Ganduje ya rushe shirinsa na rarraba masarauta -Sheikh Dahiru Bauchi

A cewar sanarwar umarnin gyaran gidan Shattima na nuna cewar na nuna cewar nan bada jimawa za’a kaddamar da sabuwar majalisar masarautar Kano wanda yayi dai-dai da dokar  data kafa majalisar sarakunan yanka ta jihar Kano wanda majalisar dokoki ta jihar Kano ta zartar a kwanakin baya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!