Connect with us

Labarai

Majalisar wakilai zata sake bincikar dawo da tallafin man fetur

Published

on

Majalisar wakilai ta ce za ta binciki sake dawo da tallafin man fetur da kuma dakile matsalolin da ke janyo karancin mai a kasar nan.

 

Shugaban majalisar Yakubu Dogara ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da mambobin majalisar wadanda suka dawo daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

 

Ya ce majalisar za ta yi aiki tukuru domin samar da mafita game da matsalar tsaro dana tattalin arziki da ke addabar kasar nan.

 

Yakubu Dogara ya kuma ce abin damuwa ne matuka yadda aka fuskanci matsalar karancin man fetur a kasar nan a karshen shekara.

 

Yana mai cewar dalilan da suka sanya suka goyi bayan kara kudin litar mai daga naira tamanin da bakwai zuwa dari da arba’in da biyar shine tabbatar musu da aka yi cewa za a cire tallafin mai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!