Labarai
Masu sarautun gargajiya na yiwa ma’aikata katsalandan- Kungiya
Shugaban Kungiyar kwadago na kamfanoni masu zaman kansu na jihar Kano Kwamared Ali Baba, ya zargi masu rike da sarautun gargajiya musamman masu unguwanni na Kano da yiwa ma’aikatan kamfanoni barazana matukar suka yi yunkurin kafa kungiya a kamfanin da suke aiki.
Kwamared Ali Baba ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin zantawarsa da wakilin Freedom Radio Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa inda ce hana ma’aikata shiga kungiya a kamfani ba komai zai haifar musu ba face bautar da su da tare da take musu hakkokinsu da walwala.
Haka kuma ya kara da cewa abun ba iya nan ya tsaya ba domin kuwa masu unguwannin su kan bi gidajen iyayen ma’aikatan suna jan kunnensu cewa su gargadi ‘ya’yansu kan kada su sake su yi maganar kafa kungiya a kamfanonin da suke aiki wanda hakan bai kamata ba.
Kwamared Ali Baba ya ce a shekarun baya zamanin marigayi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Dr Ado Bayero kungiyar ta taba kai masa kuka akan lamarin dake faruwa a kamfanonin saboda lamarin yana matukar ci musu tuwo a kwarya.
Shugaban Kungiyar kwadagon na kamfanoni masu zaman kansu ya ce akwai tarin zarge – zarge da suke yiwa masu unguwanni ciki har da zargin hada baki da masu kamfanoni cewa duk wanda za a dauke shi aiki sai an kafa masa sharadin cewa babu batun kafa kungiya a kamfani.