Connect with us

Manyan Labarai

Matashi dan shekara 20 ya nutse a kogin Bachirawa

Published

on

Wani matashi dan shekara 20 da haihuwa ya nutse a yayin da yake wanka  a kogin Bachirawa -Darewa dake yankin karamar hukumar Ungogo a nan jihar Kano

 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Malam Sa’idu Mohammad ne ya bayyana afkuwar alamarin inda ya ce matashin ya nutse a kogin ne a ranar lahadi bayan da suka je wanka.

 

Rahotanni sun bayyana  cewar wani mazaunin unguwar Malam Abdulrahma Adamu , ya ce al’amarin ya faru ne da misalin karfe 12.45 na rana, inda aka tsinci gawar matashi iliyasu, ya kara da cewa suna samun labarin suka garzaya domin ceto matashin, amma ina rai yayi halin sa.

 

Suna isa kogin da misalin karfe daya na rana ko da suka isa sai gawar matashin aka tsamo, tuni suka mikawa mai unguwar Zango Barebari Alhaji Ahmad Isa  gawar matashin.

 

A ranar 5 ga watan Satumban wannan shekara ne dai  aka sami rahoton wani matashi dan shekara 16 Shahid Lawal ya nutse a kogin na Bachirawa-ramin  Kasa dake karamar hukumar Fagge a yayin da yake wanka

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!