Labarai
Mun samar da taransifomomi guda 500 a kano – kwamshinan raya karkara
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta samar da taransifomomi guda 500 a faɗin jihar, domin samar da hasken hutar lantarki a birni da karkara.
Kwamishinan Raya karkara da bunƙasa birane Alhaji Abbas Sani Abbas ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai a ofishinsa.
Alhaji Abbas Sani Abbas ya ƙara da cewa gwamnati zata saka taransifomomin ne a kauyuka da birane da kuma yankunan da suke fuskantar matsalolin hasken lantarki a cikin kwaryar birnin Kano.
Abbas ya kuma ce ma’aikatarsa za ta samar da rijiyoyin burtsatse guda dubu biyar a kananan hukumomi 44 dake faɗin kano domin magance matsalar karancin ruwan sha.
Haka kuma kwamshinan Ya yi kira ga al’ummar jihar Kano dasu koyi dabi’ar alkinta kayan gwamnati kasancewar gwamnati tana samar da kayan ne domin cigabansu.
You must be logged in to post a comment Login